ABOUT US  |  CONTACT US
Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences
Volume-1 | Issue-02
Original Research Article
Wanda Ya Tuna Bara...: Biɗa Da Tanadi A Tsakanin Hausawa Matasa A Yau
Abu-Ubaida Sani Umar Buba, brahim Mohammad
Published : Dec. 22, 2019
DOI : 10.36348/gajhss.2019.v01i02.001
Abstract
Abstract: Wannan aiki ya mayar da hankali ne kan tasirin biɗa (nema) da tanadi (tattali) ga cigaban tattalin arziƙin Bahaushe. Takardar ta yi bitar ma’anoni da kamanci da kuma wasu bambance-bambancen da ake iya samu tsakanin kalmomin guda biyu. Bayan haka, an nazarci yadda lamarin ya ke ga Bahaushen yau. Bugu da ƙari, an yi bitar gurbin biɗa da tanadi ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. Domin binciken ya kuɓuta daga jin kunyar ilimi da masu ilimi, an bi manyan hanyoyi bincike guda biyu waɗanda da su ne aka yi amfani wajen tattara bayanai yayin binciken. Hanyoyin su ne, bitar ayyukan da suka gabata da kuma tambayoyi. An ɗora aikin kan tunanin Bahaushe na “Mai nema na tare da samu.” Binciken ya gano cewa, biɗa da tanadi ba a matsayin tasiri kawai suka kasance ba, su ne ke tallafe da tattalin arzikin Bahaushe a tarihance. A ɓangare guda kuma, tasirin zamani da sauye-sauyen yanayi ya kawo sauyi ga yadda tsarin yake a baya. Hakan kuwa ya samar da giɓi bayyananne ga tattalin arziƙin Hausawa, duk kuwa da cigaban da aka samu a ɓangare guda. A bisa haka ne takardar ke ba da shawarar cewa, a yi hoɓɓasar nazartar hanyoyin ɗinke wannan ɓaraka a matakin ɗaiɗaikun al’umma da gundumomi da kuma a gwamnatance.

Article formats

PDF (Portable Document Format) is a file format that has captured all the elements of a printed document as an electronic image that you can view, navigate read more...

A full-text database is a compilation of documents or other information in the form of a database in which the complete text of each referenced document is read more...

Contact us


Scholars Middle East Publishers,
Gold Souk, Deira, d – 24 D85,
Dubai, United Arab Emirates

+971-54-717-2569
submit.gajrc@gmail.com

Useful Links


Home
Aim and Scope
Author Guidelines
Subject Area

About Us


GAJRC (Global Acedemic Journals and Research Consortium) is an international scholar’s community which publish research paper under Scholars Middle East Publisher for open access scientific journals in both print and online publishing from Dubai, UAE. Read More Here

© GAJRC , All Rights Reserved

Developed by JM